'Yan tawaye a Sudan sun amince da dakatar da bude wuta

Sudan
Image caption Madam Valerie Amos

Shugabar hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos, ta ce 'yan tawayen Sudan sun amince da dakatar da bude wuta domin kayan agaji su kai ga farar hula.

Shugabar ta ce hakan na kunshe ne a wata wasika daga kungiyar 'yan tawayen ta Sudan Revolutionary Front wadda hadaka ce ta kungiyoyin 'yan tawaye da ke fada a yankin Darfur a yammacin Sudan da kuma jihohin Kordofan da Blue Nile wadan da ke kusa da iyakar Sudan ta kudu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fadan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye ya jefa mutane da dama cikin halin kaka-ni-kayi a Kordofan da Blue Nile inda rikicin ya shafi mutane kusan miliyan daya.