Kawancen gwamnatin Girka ya balbalce

Fotis Kouvelis, Shugaban Jamaiyar Democratic Left
Image caption Fotis Kouvelis, Shugaban Jamaiyar Democratic Left

Jam'iyya mafi kankanta a gwamnatin gamin gambizar Girka ta Democratic Left, ta tabbatar cewa za ta janye daga gwamnatin.

Sai dai shugaban ta, Fotis Kouvelis, ya yi gargadi game da gudanar da zabe kafin lokacin yinsa, kuma ya ce jam'iyyarsa za ta cigaba da goyon bayan sauye-sauyen da ake son kawowa a kasar ta Girka.

Wannan mataki dai ya biyo bayan rugujewar tattaunawar da aka yi ne kan makomar kafar yada labaran radiyo da talabijin na gwamnatin kasar, ERT.

[Wakilin BBC ya ce Idan dai jam'iyyar ta Democratic Left ta janye, gwamnati za ta samu rinjayen kujeru 3 ne kacal a majalisar dokokin kasar, abun da zai jefa kasar cikin wani halin rashin tabbas .

A makon jiya ne dai, Pira ministan kasar, Antonis Samaras ya rufe kafofin rediyo da talabijin din, a matsayin wani bangare na matakan tsimin da gwamnati ta dauka, abun da ya janyo bacin ran abokan kawancensa masu ra'ayin sauyi.