Najeriya ta yi karin haske kan jirgin saman Kenya

Jirgin sama
Image caption Jirgin sama na shawagi a sararin samaniya

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewar ta hana wani jirgin saman Kenya tashi wanda ya kai wasu Yan Najeriyar 3 da aka kora daga Kenyar,gida a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas.

Gwamnatin ta ce ta hana wa jirgin tashi ne saboda rashin bin tsarin tsaro na kasar.Manajan kula da hakokin sadarwa na kafofin sufurin jiragen sama na kasar, Yakubu Datti ne ya tabbatar da hana tashin jirgin.

Sai dai ya ki ya bayyana irin laifin tsaron da jirgin saman ya aikata.

Wannan ne karon farko da jami'an Najeriya suka ce wani abu game da hana jirgin na kenya tashi tun isarsa kasar ranar 3 ga watan Yuni.

Daya daga cikin wadanda Kenyar ta tasa keyarsu zuwa gida Najeriyar Anthony Chinedu, ya shedawa BBC cewar ba za a saki jirgin saman da ma'aikatansa ba har sai an kyale shi ya koma Kenyar.