Ambaliyar ruwa a India: Ana ci gaba da aikin ceto

Image caption Wasu da suka tsira daga ambaliyar ruwa

A arewacin India ana can ana cigaba da ƙoƙarin ceto dubban mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ta rutsa da su.

Aƙalla dai kusan mutane dari shida ne suka mutu ya zuwa yanzu.

Gwamnati ta bayyana lamarin da cewa, wani babban bala'i ne da ya aukawa kasar.

Jami'an tsaro da suka kai dauki yankunan da lamarin ya shafa suna amfani da jirage masu saukar ungulu wajen kwashe mutane.

Wasu da lamarin ya shafa tuni suka soki gwamnati da rashin kai musu dauki akan lokaci.

Can a birnin Mumbai ma, 'yan sanda sun ce mutane goma sun mutu ciki har da yara biyu lokacin da wani gini ya rufta.

Mutane dama ne ake sa ran ginin ya ritsa da su kuma babu tabbas kan dalilin rushewar ginin, amma birnin na Mumbai ya fuskanci ruwan sama mai yawan gaske a 'yan kwanakin nan.

Karin bayani