Mahara sun kashe 'yan yawon bude ido a Pakistan

Yanki mai tsaunuka a Pakistan
Image caption Yanki mai tsaunuka a Pakistan

'Yan sanda a Pakistan sun ce wasu 'yan bindiga sun hallaka akalla baki 'yan yawan bude ido Turawa su tara da kuma mai yi masu jagora a wani yanki mai cike da tsaunuka dake karkashin ikon Kashmir.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya ce 'yan bindigar wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kai hari ne a otal din da mutanen suke zaune a Diamar dake arewacin lardin Gilgit Baltsitan, kusa da sansanin Nanga Parbat, wanda ya kunshi daya daga cikin tsaunuka mafi girma a duniya.

Akwai rahotannin dake cewa mutanen sun fito ne daga kasashen China da Rasha da Ukraine.

Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari da Prime Minista Nawaz Sharif sun yi allawadai da kashe-kashen da kakkausar murya.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba