Ramphele ta kafa sabuwar jam'iyya

Image caption Mamphela Ramphele, 'yar siyasa a Afurka ta kudu

Wata wacce aka fafata da ita wajen yaki da mulkin wariyar launin fata a Afurka ta kudu ta ƙaddamar da sabuwar jam'iyyar siyasa da zata ƙalubalanci jam'iyyar ANC mai mulki a zaben da za'a yi baɗi.

Mamphela Ramphele ta fadawa gangamin magoya bayanta a Pretoria cewa, jam'iyyar ANC mai mulki ba zata iya ceto tattalin arzikin kasar ba.

Ramphele ta ce, abinda ya rage mana shi ne fata na gari da muke da shi dangane da abinda gobe ta ƙunsa, dan haka dole mu zabi abinda ya zo yau, ba wai abinda ya dade ana yin ba.

Mamhpela Ramphele tace, jam'iyyar ta za ta maida hankali ne ga yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma bunƙasa ilimi.