Mandela na cikin mawuyacin hali a asibiti

Fadar shugaban Afirka ta Kudu ta sanar cewa, tsohon shugaban ƙasar Nelson Mandela, ya shiga cikin wani mawuyacin hali a asibitin da yake kwance.

A cikin wata sanarwa, shugaba Jacob Zuma ya ce, likitocin mista Mandela na yin iyakacin ƙoƙarinsu don ganin ya sami sauƙi.

A farkon wannan watan ne aka kai Nelson Mandelan asibiti, a karo na uku a cikin wannan shekarar, yana fama da ciwon huhu.

Nelson Mandela, mai shekaru 94 a duniya, shine bakar fata na farko da ya taba zama shugaban Afirka ta Kudu.

Sanarwar da fadar shugaban ta bayar ta ce, da yammacin yau Jacob Zuma ya ziyarci mista Mandela a asibiti a Pretoria, kuma an gaya masa cewa, lafiyarsa ta taɓarɓare a sa'o'i 24 da suka wuce.

Shugaba Zuma yayi ƙira ga jama'a da su yi wa Mandela da likitocinsa addu'a.