Shugaba Putin ya ce Snowden na filin jirgin Moscow

Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Image caption Shugaba Vladimir Putin na Rasha

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce, har yanzu jami'in leken asirin nan mai gujewa shari'a, Edward Snowden, na a yankin matafiyan da ke kan hanyarsu ta wucewa na filin jiragen Moscow.

Ana dai nemansa a Amurka saboda fallasa bayanan wani shirin leken asirin bayanan jama'a na Amurka.

Da yake magana a Finland Mr Putin ya ce, zai fi masa kyau ya zabi wurin da za shi cikin hanzari.

Mr Putin ya ce zuwansa Rasha abu ne da ba a tsammata ba, kuma yana fatan ba za ta shafi dangantaka da Amurka ba.

Tun farko Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce Mr Snowden dai bai fice daga kasar Rasha ba.

Haka nan kuma China ta yi watsi da zargin Amurka na cewar ta taimaka wa Mr Snowden wajen barinsa ya bar Hong Kong.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci Rasha da ta mika Mr Snowden, yana cewa babu dalilin karin sa-in-sa tsakanin kasashen biyu.

Shi dai Mr Snowden na kokari ne na isa kasar Ecuardor inda ya bukaci a ba shi mafakar siyasa.

Karin bayani