Rashin lafiyar Mandela ya tsananta

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai

Ana cigaba da nuna damuwa a daukacin duniya musamman ma a Afrika ta Kudu, game da lafiyar tsohon Shugaban Kasar, Nelson Mandela wanda yanzu haka rashin lafiyar ta sake kamari a asibiti.

Likitocin dake duba lafiyarsa sun ce yana cikin wani mawuyacin hali.

Labarin dai yazo ne a wata sanarwa da fadar Shugaban Kasar Afrika ta Kudu ta fitar.

Mandela mai shekaru 94 a duniya ya shafe fiye da makonni biyu a asibiti, inda ake duba shi sakamakon cutar huhun da ta sake taso masa.

Shugaba jacob Zuma dai ya ziyarci Mandela a yammacin ranar Lahadi, ya kuma yi magana da likitocin dake kula da Mr. Mandela.

Daga baya ne kuma Mr. Zuma ya sake nanata kiransa ga 'yan Kasar da ma duniya baki daya, da su sanya Mr. Mandela a cikin adduo'insu.

Mac Maharaj mai magana da yawun Shugaba Zuman ya shaidawa BBC cewa "Muna son mu tabbatarwa da jama'a cewa likitoci na bakin iyakar kokarinsu, domin ganin ya samu sauki. Sai mu yi masa fatan samun sauki, amma a lokaci guda kuma ya kamata mu sani cewa yana cikin wani mawuyacin hali."

Karin bayani