Gowon ya ce za a magance matsalar tsaro

Janar Yakubu Gowon
Image caption Janar Yakubu Gowon

Yayin da ake cigaba da fama da matsalar tsaro a Najeriya, wasu dattawan kasar sun ce tilas sai jama'a sun tashi tsaye wajen baiwa hukumomi hadin kai kafin a iya shawo kan matsalar.

A cewar dattawan, irin yadda gwamnati ta yi nasarar kawo karshen yakin basasa a shekarun baya, alamu na tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriyar.

Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Yakubu Gawon mai ritaya, na daga cikin magabatan kasar dake da wannan ra'ayi.

Kuma ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC.

Janar Gowon yace kungiyar Boko Haram mai tayar da zaune tsaye, kungiya ce ta wasu mutane masu gurbata addinin Musulunci.

Ya kuma kara da cewa ba haka addinin Musulunci yake ba, domin ya san Musulmi sun yi yaki, domin ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.