Rudani game da inda Snowden yake

Ginin Ofishin jaladancin Ecuador a Mosko
Image caption Snowden ya nemi mafakar siyasa ne a Ecuador

Ana ci gaba da kila-wa-kala game da inda jami'in leken asirin Amurkar nan Edward Snowden ya ke.

Wani wakilin kamfanin jiragen saman Rasha na Aeroflot ya ce mutumin da ya fasa-kwai game da wani gagarumin aikin sa ido kan sakonnin waya da na email a Amurka, bai shiga jirgin da ya sayi tikiti ba, mai zuwa Cuba daga Mosko.

Shi ma wani dan jarida na BBC dake cikin jirgin saman ya ce bai ga Mr Snowden ba.

Mr Snowden ya isa Mosko ne daga Hong Kong inda yake boye.

A halin da ake ciki , kasar Ecuardor ta tabbatar da cewa Mr Snowden ya nemi a ba shi mafakar siyasa a can.

Ricardo Patino , ministan harkokin wajen kasar ta Ecuardor ya tabbatar da cewa sun karbi bukatar neman mafakar, kuma suna nazari a kanta.

Karin bayani