Matafiya za su ajiye kudin jingina kafin shiga Burtaniya

Theresa May
Image caption Theresa May, Sakatariyar cikin gidan Burtanioya

Hukumomin Burtaniya sun ce za su bullo da wani tsari wanda a karkashinsa za' a tilastawa matafiya ajiye kudin jingina na dala dubu hudu da dari shidda kafin su samu izinin shiga cikin kasar.

Sabon tsarin, wanda zai fara aiki daga watan Nuwamba mai zuwa, zai shafi matafiya da shekarunsu suka kama daga 18 zuwa sama, kuma kasashe 6 ne shirin ya shafa, wadanda suka hada da Najeriya da Ghana da Bangladesh da kuma India.

Hukumomin na Burtaniya sun ce matafiya daga irin wadannan kasashe suna da hadarin keta dokokin shige-da-fice na Burtaniyar.

A cewar hukumomin na Burtaniya idan ire-iren wadannan mutane suka zarta lokacin da ya kamata su kwashe a kasar, to za su yi asasar kudin jinginar da suka ajiye.

Karin bayani