An kai hari fadar shugaban Afghanistan

Hayaki na tashi daga fadar Shugaba Karzai
Image caption Hayaki na tashi daga fadar Shugaba Karzai

'Yan bindiga a Afganistan sun kai hari a fadar Shugaban kasar, abin da ba a taba gani ba tun bayan fatattakar 'yan kungiyar Taliban shekaru 12 da suka gabata.

An sami mummunar fashewar wani abu a daidai kofar shiga fadar Shugaban Kasar, kuma wani bakin hayaki ya rinka fitowa daga cikin gine-ginen da hukumar leken asiri ta CIA ke amfani da su.

Babban jami'in 'yan sanda na birnin Kabul Ayub Salangi ya gaya wa BBC cewa, wadanda suka kai harin wasu mutane ne dauke da katin jabu na shiga wurin, jami'an tsaro sun tsayar da motarsu a lokacin ne kuma suka fara bude wuta.

Jami'in yace, an kashe dukkan mutanen da suka kai harin wadanda ake jin su hudu ne, duk da yake dai har yanzu ba a riga an tantance yawan su ba.

Wani mai magana da yawun Taliban ya ce su ne ke da alhakin kai harin, sun kuma hari Otel din Asiana ne wurin da jami'an hukumar leken asiri ta CIA na Amurka ke amfani da shi.

Karin bayani