Shugaba Obama ya dauki sabon matakin takaita gurbata muhalli a kasar.

Shugaba Obama
Image caption Rage hayaki

Shugaba Obama ya bada sanarwar daukar wani sabon mataki na takaita yawan hayaki mai gurbata muhallin da ake fitarwa a Amurka.

A wani jawabi da ya gabatar a jami'ar Georgetown, Mr Obama ya kaddamar da wasu sharudda da su ne na farko da gwamnatin tarayya ta taba fitarwa kan gurbatacciyar iskar da kampanonin makamashi na Amurka ke fitarwa.

Ya ce, "A yau , domin kare 'ya'yanmu, da kuma lafiya da tsaron daukacin Amurkawa, zan umurci hukumar kare muhalli da ta kawo karshen yadda masana'antunmu na makamashi ke giurbata muhalli."

Shugaban kasar ya ce zai yi amfani da ikon da yake da shi na zartarwa, wajen ganin ana aiki da sabin dokokin.

Batun kare muhallin dai yana cikin batutuwan da shugaban ya nuna zai tunkara a lokacin yakinsa na neman zabe na farko.

Mutane da dama kuma sun ta sukarsa a kan kasa cika wannan alkawari irin yadda ya kamata.