Amnesty ta koka kan matsa wa masu luwadi

Wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar a yau ya nemi da a kawar da kyamar 'yan luwadi da kuma masu madigo.

Rahoton ya ce nuna kyama ga irin wadannan mutanen yafi yawaita ne a kasashen Afrika, kudu da sahara irin su Kenya da Afrika ta Kudu da kuma Kamaru, inda duk wani da ake tuhuma ko kuma ya bayyana kansa a matsayin dan luwadi, yake fuskantar mummunan hukunci.

Kungiyar ta ce bai kamata a hana wadannan mutanen 'yanci su na saduwa da wadanda su ke so ba.

Kasashen Afrika da dama dai na da dokokin da suka haramta wannan lamari, wasu ma sun yi sabbin dokokin hana auren jinsi daya.

A Najeriya dai majalisun dokokin kasar sun kafa dokar haramta auren jinsi daya, wadda ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ya shiga cikin lamarin.

Wani dan majalisar dokoki na tarayyar Najeriyar, Jagaba Adams Jagaba, yace kungiyar kare hakkin bil adaman ta Amnesty International ba ta isa ta hana Najeriya kafa dokokin da suka dace da al'adun jama'ar ta ba.

Karin bayani