An kashe fursunoni hudu a Najeriya

An kashe fursunonin ne ta hanyar rataya
Image caption An kashe fursunonin ne ta hanyar rataya

An rataye wasu fursunoni hudu a jihar Edo dake kudancin Najeriya, a karo na farko cikin shekaru bakwai, a cewar jami'ai.

Kungiyar karen hakkin bil'Adama ta Amnesty International, ta ce bayyanan da ta samu sun nuna cewa hukumomi sun rataye mutanen hudu, wadanda wata kotu ta yanke wa hukuncin kisa.

Rahotanni sun ambato kwamishinan shari'a na jihar Edo Henry Idahagbon na cewa, an samu fursunonin da laifin aikata fashi da makami ko kuma kisan kai ne.

Kamfanin dillancin labarai na AP kuma, ya ce mutanen sun hada da Chima Ejiofor da Daniel Nsofor da Osarenmwinda Aiguokhan da Richard Igagu.

Ragowar mutum na biyar kuma mai suna Thankgod Ebhos, ba a kai ga rataye shi ba, saboda wata tangarda da aka ce matokarar igiyar ratayewar ta gamu da ita.

An yi tur da kisan

Wata mataimakiyar darakta a kungiyar ta Amnesty International, wacce ke kula da al'amuran Afirka, Lucy Freeman, ta yi tir da hukuncin kisa.

Tana mai cewa mummunan koma baya ne ga fafutukar kare hakkin bil'Adam a Najeriya, kana ta jaddada kira ga hukumomin kasar da su dakatar da aiwatar da irinsa.

Sai dai, kwamishinan yada labarai na jihar ta Edo, Mista Louis Odion yace "Ba zan iya tabbatar da labarin ko hukumar gidajen yari ta Najeriya ta zartar da wani hukuncin kisa a gidan yarin birnin Bini ba. Ka san wannan wata hukuma ce da ke karkashin gwamnatin tarayya, ba gwamnatin jiha ba."

"Amma dai bayanin da zan iya tabbatarwa shi ne, a bara gwamnan wannan jiha ta Edo, Adam Oshimohle ya sa hannu a takardar izinin zartar da hukuncin kisa, kan wasu mutane biyu, wadanda kotu ta samu da laifi, kuma kotun koli ta tabbatar da hukuncin." Inji Mr. Odion.

Ya kara da cewa "Wadannan mutane an same su ne da aikata laifin kisan kai shekaru goma sha biyu da suka gabata, kuma aka yanke masu hukuncin kisa, amma suka daukaka kara har zuwa kotun koli."

Zartar da hukuncin kisan na jihar Edo ya zo ne kwanaki kadan bayan an ruwaito shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan na karfafa wa gwamnonin kasar gwiwa, a kan su rinka sa hannu a takardun izinin zartar da hukuncin kisa da kotuna suka yanke a jihohinsu.