Michael Jackson ya cika shekaru hudu da rasuwa

Michael Jackson
Image caption Michael Jackson

Shahararren mawakin nan wanda ya yi fice a fagen wakokin turanci da wani salon rawa, Micheal Jackson ya cika shekara hudu da mutuwa.

Micheal Jackson wanda bakar fata ne dan Amirka ya yi fice a sakamakon yadda wakokinsa da kuma rawarsa ta zama tamkar gagara misali.

Mutane da dama musamman matasa suna cigaba da nuna alhininsu ga mutuwarsa.

Yanzu haka dai solon rawa irin wanda Michael din ya kirkiro, ya zamo abin koyi ga matasa mawaka na zamani da samari da 'yan Mata.

Karin bayani