Ruwa ba ya ratsa sabuwar wayar Sony

Wayar kamfanin lataroni na Sony
Image caption Wayar kamfanin lataroni na Sony da ruwa baya ratsawa

Kamfanin lataroni na Sony ya sanar da fito da wayar komai da ruwanka mai manhajar Android wacce ruwa ba ya ratsawa, kuma ta na da fuskar da fadinta bai wuce inci 6.4 ba.

Kamfanin na tallata wayar da cewa ita ce samfurin Xperia Z Ultra mafi siranta dake da fuska mai fadi a kasuwa.

Haka kuma wayar na karbar sakon zane-zane da rubutu ta hanyar amfani da fensur ko biro mai bakin karfe tare da zabin salon runbutu.

Kamfanin ya ce yana da niyyar wayar ta ja da wayar kamfanin Samsung wanda ya yi kane-kane a sashen manyan wayoyi.

Bincike

A cewar wani binciken da masu bincike na Transparency market research ya yi ya nuna Samsung na da kashi 70 cikin dari na manyan wayoyi samfurin superphone da na Phablet a kasuwa a shekarar 2012.

Saboda wayoyin da suka samu karbuwa kamar Galaxy S3 da Galaxy Note 2.

Kuma a farkon wannan shekarar ne kamfanin ya kara fito da Galaxy S4 da Galaxy Mega mai fadin fuska inci 6.3.

Sony dai na da wayar mai inci biyar samfurin Xperia Z ta asali wadda ya fitar a watan Janairu.

Wannan da ya fitar yanzu mai biye wa waccan wato Ultra, an kaddamar da ita ne a bajekolin wayoyi a Shanghai.

Za a sayar da sabuwar wayar a China da Indonesia da kuma Singapore a watan Yuli, sai kuma a nahiyar Turai a watan Satumba.