Masar: An baza ƙarin dakaru

Rundunar sojan ƙasar Masar ta tura ƙarin dakaru da motoci masu sulke zuwa wasu muhimman wurare a birane da dama na ƙasar, gabanin zanga zangar da 'yan adawa suka shirya gudanarwa ranar Lahadi.

'Yan adawar dai zasu yi kira ne ga shugaba Morsi ya yi murabus.

Tuni aka fara samun arangama tsakanin magoya baya da masu adawa da shugaba Morsi.

An kashe mutane biyu, an kuma raunata wasu sama da dari biyu a garin Mansoura dake arewacin kasar.

Rikicin siyasar ya sa mutane da dama a kasar ta Masar sayen kayan masarufi da ma man petur su jibge a gida, gabanin zanga zangar ta ranar Lahadi.