Za a kai agajin abinci a jihohi uku na arewa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta kai kayayyakin agaji na abinci ga dimbin mutane da tashin hankali ya shafa a jihohi uku na arewacin kasar da aka kafawa dokar ta-baci a watan da ya gabata, inda rahotanni ke cewa jama'ar yankin na fama da kuncin rayuwa.

Kazalika, gwamnatin ta ce, bayan na ta kayayyakin abincin, akwai kuma masu hannu da shuni da suka bayyana cewa za su ba da na su taimakon.

Saboda dalilai na tsaro, ana tababar ko kayan agajin nan za su fitar da mutanen yankin daga kangin na rashin abinci musamman ganin kuma da wuya idan za su samu sukunin yin noma a bana.

Ministan ayyukan gona na Nijeriya Dr Bukar Tijjani a hira da BBC ya bayyana cewar lamarin ba zai kazance ba yadda ake hasashe, manoma za su samu sukunin yin noma.

Karin bayani