Najeriya na korar 'bakin haure'

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar shige da fice a Najeriya ta tashi tsaye wajen kama 'bakin haure' a kasar.

A jahar Kaduna, hukumar ta gudanar da wani samame a kananan hukumomi uku, inda ta kama 'yan kasashen waje sama da 150, akasarin su yan asalin jamhuriyar Nijar.

Hukumar kula da shige da ficen ta ce, ta kai samamen domin kama bakin da ke zaune a kasar ba tare da takardar izinin zama ba.

Ta ce ta dauki matakin ne saboda matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar, musamman a yankin arewa.

Tuni dai hukumar ta ce ta maida 'yan Nijar din140 zuwa gida, duk da cewa a jiya ne kawai ta yi wannan kamen.

Kungiyar 'yan asalin Nijar a Najeriyar ta nuna rashin jin dadinta game da kame-kamen.

Ta ce an yi irin wadannan kame-kamen a wurare irinsu Katsina da Rivers da Edo da kuma Shagamu.

Kungiyar 'yan Nijar din ta ce, ya kamata hukumomin tsaron kan iyaka su yi kokarin maida bakin hauren gida tun su na kan hanya, ba wai sai bayan sun kwashe dogon lokaci suna zaune a Najeriyar ba.