Najeriya ta yi martani ga ziyarar Obama

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Yayin da shugaban Amurka Barrack Obama ya fara ziyara a wasu kasashen Afrika uku, gwamnatin Najeriya ta ce rashin zuwansa Najeriya ba zai bata dangantaka tsakanin kasashen biyu ba.

A ranar Laraba ne shugaba Obama zai fara ziyara zuwa kasashen Senegal da Tanzania da kuma Afrika ta Kudu.

Wannan dai ita ce ziyararsa ta biyu zuwa nahiyar Afrika, tun bayan da ya dare karagar mulki a matsayin shugaban Amurka.

Najeriya a wannan karon ma ba ta cikin kasashen da Shugaba Obama zai ziyarta, abin da masharhanta ke ganin koma-baya ne ga kasar, saboda rashin ingantaccen mulki na democradiyya.

Sai dai kuma yayin da ake ganin haka hukumomin Najeriyar sun mayar da martani da cewa ba lallai ba ne sai Mr Obama ya ziyarci kasar.

Ministan watsa labaran kasar Mr. Labaran Maku, ya ce kasashen biyu na da jakadu, don haka duk wata hulda, za a iya gudanar da ita a tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani