Sudan ta Kudu za ta gina bututan mai biyu

Mahakar mai ta Sudan ta Kudu
Image caption Sudan ta Kudu na da kashi 75 cikin dari na arzikin man da kasashen biyu ke da shi a da

Sudan ta Kudu ta kusa cimma burinta na gina bututan mai biyu, wandanda za ta dinga fitar da mai zuwa gabashin Afrika.

Shugabannin kasashen Uganda da Kenya da kuma Rwanda sun aminci da gina bututan mai guda biyu zuwa gabashin Afrika daga Sudan ta Kudu.

Daya daga cikin bututan za a gina shi daga Sudan ta Kudu zuwa birnin Lamu mai tashar jiragen ruwa na Kenya, yayin da dayan kuma za a gina shi ya bi ta Rwanda zuwa Mombasa.

A halin yanzu dai Sudan ta Kudu na fitar da man ta ta cikin jamhuriyyar Sudan, kuma ana samun tsaiko sosai saboda rashin jituwar dake tsakanin kasashen game da batun kudin da za a biya da kuma sha'anin tsaro.

Ministan harkokin wajen Uganda, Sam Kuteso ne ya tabbatar da rattaba hannu a kan yarjejeniyar, tsakanin shugabannin kasashen uku.

A makon da ya gabata ne shugaban Sudan Omar Al-Bashir ya yi barazanar dakatar da tura man da Sudan ta Kudu ke yi ta cikin kasarsa, har sai Sudan ta Kudu ta daina taimakawa 'yan tawayen dake ayyukansu a tsallaken bakin iyakokin kasashen.

Ko da yake Sudan ta Kudu ta musanta zargin, amma ita ma ta zargi Khartoum da taimaka wa masu tada kayar baya a cikin Sudan ta Kudu.