Amurka: Doka ta amince da auren jinsi guda

A wani hukunci mai tasirin gaske, kotun ƙolin Amurka ta soke dokar kare Aure, wadda ta hana gwamnatin tarayya amincewa da auren jinsi guda.

Kotun ta ce dokar ta ware 'yan luwadi daga ba su kariyar da ake ba sauran jama'a.

An rika tafi da sowa a gaban kotun bayan yanke hukuncin.

A ƙarƙashin wannan hukunci mazan da suka auri maza ko matan da suka auri mata a jihohi goma sha biyu inda aka amince da irin wannan aure, a yanzu zasu riƙa samun tallafin gwamnatin tarayya daidai da na miji da mata.

Shugaba Obama yayi marhabin da hukuncin Kotun kolin Amurkar, yana mai cewa dokar kare Auren ta mayar da ma'aurata 'yan luwaɗi da maɗigo saniyar ware.