Takaddama kan mutanen da suka mutu a Baga

An kona gidaje da dama a rikicin Baga
Image caption An kona gidaje da dama a rikicin Baga

Wasu 'yan Majalisar dattawan Najeriya na takaddama a kan rahoton da wani kwamitin majalisar ya gabatar, game da asarar rayukan da aka yi a garin Baga na jihar Borno.

Rahoton dai ya ce an kambama adadin mutanen da suka mutu, a dauki-ba-dadin da sojoji suka yi da 'yan kungiyar jama'atu ahlusSunnah lidda'awati wal jihad da wasu ke kira boko-haram.

Sai dai wasu 'yan majalisar sun ce rahoton yana da rauni, saboda ya gaza wajen fito da ainihin adadin mutanen da suka mutu.

A watan Aprilun da ya wuce ne jami'an tsaro suka yi artabu da 'yan kungiyar ta boko haram a Baga, inda aka cinnawa gidajen mazauna garin wuta, abin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

An dai fitar da al'kaluma masu karo da juna game da adadin wadanda suka mutu, saboda sojoji sun ce mutum 37 ne suka mutu, yayin da al'ummar gari da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'dama ke cewa adadin ya kai kusan 200 ko fiye da haka.

Ricikin na Baga dai ya janyo hankalin kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa, kamar Amnesty international.