Obama ya ce ba zai dauki hoto da Mandela ba

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela
Image caption Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela

Shugaba Barack Obama wanda ya doshi Afrika ta Kudu ya shashantar da jita jitar cewar mai yiwuwa ya ziyarci Nelson Mandela a asubiti.

Mr Obama ya ce ba zai so yayi shisshigi a daidai lokacin da iyalan Mr Mandela suka damu da halin da yake ciki ba.

Ya ce babu wata bukata ta samun damar daukar hoto.Mr Obama ya ce babban sakon da zai aikewa iyalan Mr Mandela shi ne babbar godiya saboda shugabancinsa da kuma cewar jama'ar Amurka na tare da su.

A halin da ake ciki kuma tsohuwar matar Mr Nelson Mandela, Winnie, ta yi kira ga kafofin watsa labarai da su guji abunda ta kira jita jitar rashin tunani game da halin da yake ciki.

Da take magana a wajen gidan da ita da Mr Mandela suka taba zama a Soweto, ta ce iyalan nasa ba su san cewar suna da masoya matuka a irin wannan hali da suke ciki ba.

Jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta yi watsi da masu sukar lamiri wadanda ke cewa tana amfani da kafofin yada labarai domin cimma wata manufa ta siyasa gabanin zabe da za'ayi shekara mai zuwa abinda ya sa take amfani da kafofin yada labaran wajen maida hankali akan lafiyar Nelson Mandela.

Kakakin jami'iyyar ta ANC Jackson Mthembu ya ce, amince da bukatar kafofin yada labarai na duniya a kan lafiyar Mandela.

Tun farko dai Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma ya ce Mr. Nelson Mandela ya dan samu sauki a daren jiya, amma har yanzu yana cikin wani mawuyacin hali.

Shugaba Jacob Zuma ya fadi hakan ne, bayan ya kai ziyara wajen Nelson Mandelan a asibiti tare da ministan tsaron kasar.