An kashe mutane 32 a Jihar Filato

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 32 a wani tashin hankalin da aka yi yau a Karamar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato -- jihar da ta dade ta na fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.

Tashin hankalin dai ya faru ne bayan satar daruruwa shanun Fulani makiyaya a Karamar Hukumar Shendam mai makwabtaka, inda kuma aka ce barayin sun kai shanunm a Karamar Hukumar Langtang ta Kudun.

Mutanen yankin na Langtang dai na zargin Fulani ne da kai hari a yankin nasu da sunan bin sawun shanunsu, amma Fulanin sun musanta hakan.

Sun kuma ce su na jiran su ga matakin da hukumomi za su dauka game da shanun nasu da aka sace.

Tashin hankalin dai ya faru ne a kauyukan Magama da Karkashi da kuma Bolgan, inda aka kona kauyukan, aka kuma kashe mutane da dama.

Karin bayani