Kamaru: 'Yan majalisa sun yiwa ministoci tambayoyi

Image caption Paul Biya, shugaban Kamaru

A Kamaru 'yan majalisar dokoki sun yiwa wasu ministoci tambayoyi dangane da yadda wasu al'amurra suke gudana a cikin kasar.

Dangane da hakan ne kuma ministocin sufuri da kuma na harkokin cikin gida suka amsa wasu tambayoyi akan wasu abubuwa da suka shafi ma'aikatunsu.

Tambayoyin dai sun haɗa ne da akan batun sayen wani jirgi daga kasar China da ake da fargaba dangane da ingancinsa, da kuma yawaitar da ƙungiyoyin addini suke yi a kasar.