Tashin hankali na ci gaba da bazuwa a Masar

Masar
Image caption Barkewar tarzoma a Masar

Amurka ta gargadi 'yan kasarta da kada su kuskura su yi tafiya zuwa Masar sannan kuma ta bukaci dukkanin jami'anta na jakadanci da ayyukansu ba su zama na dole ba da su bar kasar, yayin da wutar tashin hankali ke kara ruruwa a kasar.

An bada rahotannin mace mace da raunuka a dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin magoya bayan shugaba Mohammed Morsi da na 'yan adawa, yayin da ake shirin bikin cika shekara daya da hawan shugaban mulki gobe Lahadi.

Jami'an gwamnatin Masar din sun ce daya daga cikin wadanda suka rasa ransu wani ba Amurke ne a birnin Askandariya.

Masu aiko da labarai sun ce 'yan kasar ta Masar na fargabar cewa rikicin zai iya kazanta,

lamarin da ya sa wasu tuni suka shiga tara kayan abinci da mai.