Matsayin Najeriya a kan batun kare hakkin bil'adama

A Najeriya yau ne ake kammala taron masu ruwa da tsaki kan harkokin 'yancin bil Adama, da yadda za a yi nazari kan rahoto na biyu da za a sake mikawa Majalisar Dinkin Duniya game da matsayin Najeriyar akan kare hakkin bil adama.

Majalisar Dinkin Duniyar ce ta umarci kasashen duniya da su aike da matsayinsu da kuma al'amuran da ke damunsu kan batutuwan da ke tasowa a duniya game da 'yancin dan adam.

Najeriyar dai ta amince da 30 daga cikin 32 na kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin bil Adaman .

Batun auren jinsi daya da hukuncin kisa dai sune biyu daga cikin kudurorin da Najeriyar ta ce ba ta lamunta da su ba .