Obama ya jinjinawa Mandela

  • 29 Yuni 2013

Shugaba Obama ya jinjinawa Nelson Mandela bayan ya gana da iyalan jagoran yaƙi da wariyar launin fata mai fama da rashin lafiya a Johannesburg, haka kuma yayi magana da uwargidan Mandela, Graca Machel wadda ke gefen gadonsa na asibiti a Pretoria.

Shugaba Obama ya kuma yabawa Mandela yana cewa, irin halayya ta gari da ƙarfin hali da yake nunawa abin koyi ne ga kowa da kowa.

Shugaba Obama yayi waɗannan kalamai ne a birnin Pretoria bayan ya gana da shugaba Jocob Zuma.

Ziyarar Obaman a Afurka ta kudu wani bangare ne na ƙoƙarin inganta hulɗar kasuwanci, duk da cewa batun rashin lafiyar Mandela ya ma kusan shafe maƙasudin ziyarar.