An kai Dahir Aweys birnin Mogadishu

A Somalia yanzu haka dai daya daga cikin manyan jagororin kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Al Shabaab yana hannun jami'an tsaron kasar, a birnin Mogadishu.

Har yanzu dai ba a tantance ba ko Hassan Dahir Aweys ya mika wuya ne ga dakarun gwamnati ko kuma ya balle ne daga kungiyar ta Al Shabaab.

Jiya juma'a ne dai majalisar dinkin duniya tace jigo a kungiyar ta Al Shabaab Hassan Dahir Aweys ya mika kansa ga dakarun gwamnati, amma dattawan haularsa sun musanta hakan.

Shi dai Hassan Dahir Aweys yana cikin jerin mutanen da majalisar dinkin duniya da kuma Amurka suka ce, 'yan ta'adda ne.