Shugaba Obama ya isa kasar Afrika ta Kudu

Obama visit
Image caption Shugaba Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama na shirin ganawa da takwaransa na Afrika ta Kudu, a ziyarar da ya ke a kasar wadda damuwa kan rashin lafiyar Nelson Mandela da aka kwantar a asibiti kusan makwanni uku ya kankane.

Barack Obama wanda ya bayyana matukar godiyarsa ga shugabancin Nelson Mandela kan irin yadda ya karfafawa mutane da dama guiwa a duniya,

ya kawar da rade radin da ake yi game da cewa kila zai ziyarci tsohon shugaban Afrika ta Kudun a asibiti, inda ya ce babu bukatar neman daukar hoto da tsohon dan yaki da mulkin wariyar launin fatar.

Yayin ziyarar tasa Mr Obama zai gana da dalibai a garin Soweto sannan kuma zai je dakin kurkukun da Mandela ya zauna a tsibirin Robben.

Haka kuma zai yi kokarin habaka dangantakar kasuwanci da Afrika ta Kudun a matsayin hanya ga sauran kasashen Afrika da ke kudu da hamadar Sahara