Navy Pillay na ziyara a Kamaru

Navy Pillay,Kwamishinar kula da yan gudun hijira
Image caption Navy Pillay,Kwamishinar kula da yan gudun hijira

Babbar Kwamishiniyar Majalisar dinkin duniya mai kula da kare hakkokin Bil Adama, Navy Pillay, ta sauka a Kamaru inda ta kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Kwamishiniyar za ta gana da Shugaban Kasa Paul Biya da kuma wasu manyan jami'an Gwamnati da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu domin su tattauna batutuwan da suka shafi kare hakkokin Bani Adam a Kamaru.

Navy Pillay tana wannan ziyara ne kwanaki kadan bayan kungiyar Amnesty International ta fidda wani rahoton da yace, Kamaru na cikin kasashe 38 da suke taka hakkokin 'yan luwadi da kuma 'yan madigo.