Masar: Ana ci gaba da zanga zanga

Masu zanga zanga a Masar
Image caption Masu zanga zanga a Masar

A birnin Alkahira da ma wasu biranen kasar Masar dubban mutane ne suka fito zanga-zangar kira ga shugaba Muhammad Morsi yayi murabus, yayin da yake cika shekara guda akan mulki.

Yanzu dai masu zanga-zanga sun mamaye hanyar da ta kai ga fadar shugaban kasar dake birnin Alkahira, yayin da kuma a dandalin Tahrir babu masakar tsinke, domin kuwa anyi gangamin da rabon da a ga irinsa tun shekara ta 2011 lokacin da aka kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Ana dai gudanar da zanga zanga galibi cikin lumana, to amma an kaiwa hedikwatar jama'iyar yan uwa musulmi ta Shugaba Mursi hari a Alkahira, kuma an kashe mutum daya a wani artabu tare da magoya bayan gwamnati a kudancin babban birnin.

Shugaba Mursi dai shi ne shugaban Masar na farko da aka zaba, amma masu zanga zanga na zarginsa da saka manufofin jama'iyarsa a kan na kasa.