Yansanda a Senegal sun tsare Hissene Habre

Hissene Habre, tsohon Shugaban Chadi
Image caption Hissene Habre, tsohon Shugaban Chadi

Yansanda a Senegal sun kama tsohon Shugaban Chadi, Hissene Habre, wanda ake zargi da kashe dubban masu adawa da shi a shekarun alif dari tara da tamanin.

Lauyan Hissene Habre, El Hadji Diouf, ya ce yansandan kwantar da tarzoma sun dauke shi daga gidansa a Dakar zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.

A ranar alhamis, a zangon farko na ziyararsa a Afrika, Shugaba Obama ya yabawa kokarin gwamnatin Shugaba Macky Sall na gurfanar da Hissene Habre don yi masa shari'a.

Tsohon Shugaban na Chadi ya tsere zuwa Senegal ne bayan da aka hambarar da shi a 1990.

A bara kotun manyan laifuka ta duniya ta umurci Senegal da ta gurfanar da shi ko kuma ta tasa keyarsa domin yi masa shari'a a kasashen waje.