An kai hari a gidan yarin garin Akure a Najeriya

Wani gidan yari a Najeriya
Image caption Wani gidan yari a Najeriya

A Najeriya fursunoni 175 ne rahotanni suka ce sun tsere daga gidan yarin garin Akure dake jihar Ondo bayan da wasu 'yan bindiga sun kai hari a gidan.

Sai dai Shugaban hukumar gidan yari a Jihar Mr Tunde Olayiwola ya ce fursunoni 75 ne suke da tabbacin sun tsere.

Ya zuwa yanzu dai ba tantance ko su waye suka kai harin da kuma ko mecece manufarsu ba.

Rahotanni sun ce yan bindigar sun yi amfani da nakiyoyi wajen fasa kofar shiga cikin gidan yarin, bayan da suka yi musayar wuta da gandirobobin dake aiki a gidan.

Rundunar Yansanda ta jihar Ondo ta tabbatar da afkuwar lamarin , amma ba ta ce ko harin yana da nasaba da wani aiki na ta'addanci ba.

Hukumomin gidan yarin sun ce wasu jami'ansu na asubiti yanzu haka na samun magani.