Uganda: Mutane 29 sun mutu

Image caption Kampala birni ne da ya sha fama da annoba iri iri

A Kampala, babban birnin Uganda mutane akalla ashirin da tara sun hallaka sakamakon wata gobara da ta samo asali daga wani hatsari da ya hada da tankar man petur.

Wasu mutanen talatin kuma sun samu munanan raunuka.

'Yan sanda sun ce, yawacin mutanen dai sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka tunkari wurin da tankar manpetur din tayi hatsari domin kwasar man da ya malala.

Yanzu dai gwamnati tace, za'a yi amfani da fasahar gwajin kwaoyoyin halitta na DNA domin gane mutanen, saboda sun kone kurmus ta yadda ba za'a iya gane kamanninsu ba.

'Yan sanda sun ce, ana sa ran yawan wadanda suka mutu zai ƙaru, saboda wadanda suke asibiti sun samu munanan raunuka.