An yi taho-mu-gama a Brazil

Image caption Masu zanga-zangar na kokawa game da cin hancin da kasar ke fama da shi

A kasar Brazil, an yi taho-mu-gama ranar Lahadi a tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a kusa da filin wasan kwallon kafa na Maracana da ke Rio de Janeiro bayan Brazil ta lashe kofin gasar nahiyoyi inda ta doke Spain da ci uku ba ko daya.

Masu zanga-zangar sun yi ta jifa da duwatsu ya yin da 'yan sanda suka mayar da martani da hayaki-mai-sa-hawaye.

An dai shafe makwanni ana zanga-zanga a kasar a kan cin hanci da rashawa, da karancin abubuwan more rayuwa da kuma makudan kudaden da kasar za ta kashe a wasan cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2014.

Shugabar kasar, Dima Rouseff, ba ta halarci wajen wasan ba saboda jifan da aka yi mata a lokacin bude gasar makwanni biyu da suka gabata.

Karin bayani