Ana ci gaba da zanga-zanga a Masar

Image caption Masu zanga-zanga sun kwashe dare suna gudanar da ita

Daruruwan 'yan kasar Masar sun kwashe daren ranar Lahadi suna zanga-zanga a birnin Alkahira, suna neman shugaba Mohammed Morsi mai kishin Islama ya yi murabus, shekara daya bayan hawansa kan karagar mulki.

Hanyar zuwa fadar shugaban kasar ta cika makil da masu zanga-zanga, yayin da dafifin mutanen da ke dandalin Tahrir ya kasance taron jama'a mafi girma tun juyin-juya halin shekarar 2011.

Magoya bayan shugaba Morsi ma na yin tasu zanga-zangar a wani wurin na daban a Alkahira.

Wani rahoto ya bayyana cewa mutum daya ya mutu a Alkahira, lokacin da masu zanga-zangar suka kai hari kan ofishin jam'iyar 'yan uwa musulmi, Muslim Brotherhood ta shugaba Morsi.

Kazalika mutane hudu sun rasa rayukansu a lardin Assiut.

Jami'ai sun ce fiye da mutane dari biyu ne suka samu raunuka sakamakon zanga-zanga a fadin kasar.

Karin bayani