Faransa ta gargadi Amurka akan leken asiri

Francois Hollande na Faransa
Image caption Ana zargin Amurka da aikin leken asirin jama'a

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya ce ya kamata Amirka ta daina leken asiri a kan Tarayyar Turai nan take.

Shugaban ya ce kasashen Turai ba zasu amince da irin wannan halayya ba a tsakanin kawaye.

Ya ce 'da zarar Faransa, da ma Tarayyar Turai sun sami tabbaci daga Amirkan cewa, ta daina leken asirin, to muna iya shiga sasantawa da musayar bayyanai a fannoni dabam-dabam tare da ita'.

Kafofin yada labaran Turai ne suka bayyana zargin cewa, hukumomin leken asirin Amirka sun rika sa ido kan kawayenta.

Tun farko Sakataren harkokin wajen Amirkan, John Kerry, ya ce ba sabon abu ne ba, kasa ta tattara bayyanan sirri don tsaron kanta.

Karin bayani