Majalisar Dinkin Duniya ta kai soji Mali

Dakarun majalisar dinkin duniya sun isa Mali
Image caption Dakarun majalisar dinkin duniya sun isa Mali

Rundunar kasa da kasa da Afrika ke jagoranta a Mali, wato AFISMA ta mika ragamar iko ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Aikin zaman lafiyar a Mali shi ne aiki mafi girma na zaman lafiya da Majalisar ta fara.

Dakarun yammacin Afrika na AFISMA, kimanin 6000 dake tabbatar da zaman lafiya a Malin, za su koma karkashin ikon majalisar.

Sai dai ba dukkaninsu bane za su koma karkashin Majalisar.

Aikinsu na farko shi ne tabbatar da tsaro, kafin zaben shugaban kasar Malin da za a yi a karshen wannan watan.

Wasu sojojin Faransa ma za su cigaba da kasancewa a kasar.

A watan Janairun da ya wuce ne dakarun Faransar suka je Malin, domin yakar masu kishin Islama da Abzinawa 'yan tawaye, wadanda suka mamaye arewacin kasar.