Ma'aikatan mai sun soma yajin aiki a Najeriya

Gidan mai a najeriya
Image caption An soma ganin dogayen layukan mai a Najeriya

A Najeriya, kungiyar kananan ma'aikatan mai da iskar gas ta fara wani yajin aiki na kwana uku da nufin jan hankalin gwamnati da wasu kamfanonin mai don a biya musu wasu bukatun 'ya'yan kungiyar.

Kungiyar dai na neman gwamnati ta sa baki dangane da yadda manyan kamfanonin mai ke sarrafa mambobinta.

Shugabannin Kungiyar kananan ma'aikatan mai da iskar Gas ta Najeriyar sun bayyana cewa sun bi hanyoyin lalama har hakurinsu ya gaza ba tare da samun biyan bukata ba, don haka ne suka fara yajin aiki na gargadi.

Bukatun kungiyar sun hada da neman a tilasta wa wasu manyan kamfanonin mai na waje, wato da AGIP da Shevron da kuma Shell su kyale kananan ma'aikatansu shiga kungiyar ta yadda za ta kare musu hakokinsu.

Kazalika kungiyar na neman kungiyar masu manyan motoci ta kasar wato NARTO ta kara wa matuka motocin albashi.

Harwayau kungiyar ta nemi mahukunta a Najeriya da su hanzarta gyara hanyoyin mota a kasar sakamakon tabarbarewar da suka yi, lamarin da ke haddasa hadari.

Tuni dai wannan yajin aiki ya fara yin tasiri.

Karin bayani