"Barazanar aikata kisan kare dangi" a Homs na Syria

Ruwan bama-bamai a Homs
Image caption Ruwan bama-bamai a Homs

Kasashen Larabawa na yankin tekun Pasha sun bukaci kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya da yayi taron gaggawa, domin hana abinda suka kira, barazanar aikata kiran kare dangi a birnin Homs na Syria.

Majalisar hadin kai ta kasashen yankin tekun Pashar - wadda ta hada da Saudiyya da Qatar - ta ce, musamman ta damu kan yadda mayakan Hezbollah ke yaki kafada-da - kafada da sojojin gwamnatin Syria.

Tun ranar Asabar ce dakarun shugaba Assad na Syriar, suka kaddamar da wani babban farmaki a kan 'yan tawaye a muhimmin garin Homs na tsakiyar kasar.

Karin bayani