Kotu a Senegal ta tuhumi Hissene Habre da laifukkan yaki

Hisne Habre
Image caption Hisne Habre

Wata kotu ta musamman a Senegal ta tuhumi tsohon shugaban Chadi Hissene Habre da aikata laifukkan yaki, da na cin zarafin bil'Adama da kuma azabtarwa.

Wani alkali ya bada umurnin a ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da za a fara yi masa shari'a.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun kiyasta cewa an kashe mutane kimanin dubu arba'in a kasar ta Chadi, a lokacin mulkin kama-karya na Mr Habre na tsawon shekaru takwas, har zuwa 1990.

Ranar Lahadi ne aka kama Mr Habre, wanda shekaru ashirin da biyu kenan yana zaune a kasar.

Shari'ar zata kasance mai muhimancin gaske a tsarin shari'a na Afurka, --kasancewar shi ne karon farko da wani tsohon shugaban kasar Afurka zai fuskanci tuhumar aikata laifukkan yaki a wata kasa ta Afurka.