Ana shirin bikin ranar haihuwar Mandela

Asibitin da Mandela ke kwance
Image caption Asibitin da Mandela ke kwance

Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya shaida wa 'yan kasar cewa su fara shirye-shiryen bikin zagayowar ranar haihuwar Nelson Mandela da za a yi ranar 18 ga watan nan.

Tsohon shugaban kasar wanda zai cika shekaru 95 a ranar, na kwance magashiyyan a wani asibitin dake Pretoria.

A ranar 8 ga watan Yuni ne dai aka kwantar da shi a asibitin, bayan cutar huhun da yake fama da ita ta sake tashi.

Jawabin na shugaban kasar na zuwa ne bayan tsohuwar matar Mandela ta soki gwamnatin ANC da daukar hoton bidiyon Mr. Mandela a gidansa a watan Aprilu.

Hoton wanda aka dauka a lokacin wata ziyara da wani kusa a ANC ya kaiwa Mandelan, na nuna fuskarsa ba murmushi kuma kamar yana fama da jiri.

Winnie Madikizela-Mandela ta shaidawa gidan talabijin na ITV cewa "A hakikanin gaskiya ban san yadda zan bayyana rashin jin dadin da iyalansa suka ji ba, kuma abu ne wanda rashin nuna damuwa ne kawai zai sa wani ya yi hakan."

Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta kare kanta da cewa, ba a dauki hoton bidiyon domin a nuna wa jama'a ba.

A ranar Litinin ne shugaba Zuma ya fitar da sanarwa, inda yake tunasar da 'yan Afrika ta Kudu da su fara shirye-shiryen bikin zagayowar ranar haihuwar Madiba.