Snowden: An hana jirgin shugaban Bolivia shiga Turai

Image caption Gwamnatin Bolivia ta ce Snowden ba ya cikin jirgin shugaban kasar.

Gwamnatin Bolivia ta ce an hana jirgin da ke dauke da shugaban kasar, Evo Morales, shiga sararin samaniyar wadansu kasashen Turai saboda zargin da aka yi cewa tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin Amurka, Edward Snowden, yana cikinsa.

Jirgin dai yana kan hanyarsa ne daga Moscow zuwa La Paz, yayin da katsahan aka hana shi damar ketawa ta sararin samaniyar Faransa da Portugal.

An dai sauyawa jirgin hanya ne zuwa Vienna inda ya sauka a can.

Ministan harkokin waje na kasar Bolivia, David Choquehuanca, ya ce jita-jitar da aka watsa cewa Mista Snowden yana cikin jirgin ba ta da tushe.

Ya kara da cewa rayuwar shugaba Morale ta fuskanci barazana saboda tursasawa jirgin sauka da aka yi.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Austria ya ce Mista Snowden ba ya cikin jirgin.

Karin bayani