Wa'adin soji ya janyo dar - dar a Masar

Masu bore a kasar Masar
Image caption Morsi ya umarci 'yan kasar da su kare juyin-juya halin da aka yi

Ana cikin zaman dar-dar a kasar Masar, yayin da wa'adin da sojoji suka baiwa shugaba Morsi na warware rikicin da ya janyo mutuwar mutane 16 a daren Talata ke karewa.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar ta ce mutane goma sha shida ne suka mutu a daren ranar Talata sakamakon wata taho-mu-gama da aka yi a wajen da masu gangamin goyon bayan shugaba Mohammed Morsi ke gudanarwa a birnin Alkahira.

Ta kara da cewa kimanin mutane dari biyu ne suka samu raunuka sanadiyar hargitsin.

Kamfanin dillancin labarai na Masar ya ambato ministan ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, Mostafa Hamed, na cewa mutane dai-dai ne suka mutu a Beni Suef, da Askandria, da Kafr al-Sheikh da Fayoum.

Haka kuma a cewar ministan, mutane uku sun mutu a Assiut, kana tara suka mutu a Alkahira, cikinsu har da mutum guda da ya mutu a fadar shugaban kasar, da kuma mutane takwas da suka mutu a kusa da ofishin jam'iyar 'yan uwa musulmi.

Sojoji na shirin kafa gwamnatin rikon-kwarya

Mista Hamed ya kara da cewa an sallami dukkan mutanen da suka samu raunuka daga kananan asibitocin da aka kai su don karbar magani, koda yake har yanzu a cikinsu akwai wadanda ke bukatar zuwa asibitin domin a ci gaba da duba su.

Yawancin mutanen sun samu raunuka ne sakamakon kujewa da karyewar da suka yi, yayin da wadansu kuma suka samu raunuka sanadiyar harbin bindiga.

A gefe guda kuma, shugaba Morsi ya jaddada matsayinsa na kare gwamnatinsa ko ana ha-maza-ha-mata, yana mai cewa ba za ta sabu ba dangane da wa'adin kwanaki biyu da soji suka bai wa 'yan siyasar kasar domin magance rikicinta.

Majalisar Koli ta sojin kasar ta ce a shirye sojin suke su ceto Misrawa daga wadanda ta kira 'yan ta'adda, koda kuwa za su rasa rayukansu.

Wata majiyar sojin ta nunawa BBC takardun da ke bayyana cikakken tsarin da sojin za su bi wajen kafa gwamnatin rikon-kwarya wacce za ta yi fatali da kundin tsarin mulkin kasar da ake ka-ce-na-ce a kansa, kana ta rushe majalisar dokoki, wacce masu kishin Islama suka mamaye.

Karin bayani