Masar: Wa'adin da aka ba Morsi ya cika

A Masar, wa'adin da sojojin kasar su ka baiwa Shugaba Mohammed Morsi da 'yan adawa su warware matsalar siyasar kasar ya cika.

Dubun dubatar masu zanga-zangar da suka hallara a Dandalin Tahrir a Alkahira sun yi ta shewa da wa'adin ya cika.

Magoya bayan shugaban kasar da na masu adawa da shi sun yi dafifi a wasu sassan birnin ma.

Mr Morsi ya sake nanata cewa ba zai yi murabus ba.

Ya ce gwamnatin gamin-dambiza za ta iya zama wani mataki na warware matsalar siyasar kasar Masar din.

Sojoji na tattaunawa da shugabannin gwamnati da na 'yan adawa; kuma ana sa ran cewa za su bada sanarwa bayan kammala taron.

Jiya da dare, a cikin wani jawabi dake nuna bijirewa, Shugaba Morsi ya ce ba zai yi murabus ba.

A daren jiyan akalla mutane 16 sun hallaka a taho-mu-gamar da aka rika yi.

Karin bayani