Sojoji sun sauke Shugaba Morsi na Masar

Dafifin jama'a a dandalin Tahrir
Image caption Dafifin jama'a a dandalin Tahrir

Shugaban rundunar sojan Masar ya bayyana a gidan talabijin din kasar, inda ya bayyana shirin sojojin na fitar da kasar daga cikin rudanin siyasar da ta shiga.

Ya ce, za a jingine tsarin mulkin kasar na dan wani lokaci.

Kuma babban alkalin kasar shi ne zai jagoranci Masar din, na wucin gadi, har zuwa lokacin da za a gudanar da sabbin zabubbukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Shugabannin addini da na soja ne suka kewaye Janar Abdul Fattah Al-Sisi, yayin da yake jawabin nasa.

Shugaban addinin Musulunci mafi girma a kasar, Sheikh din Masallacin Al Az-har, da kuma shugaban cocin Kipdawa ko kuma Coptic, su ma sun yi jawabi bayan Janar Al-Sisi, inda suka kawo goyon bayansu ga shirin rundunar sojan kasar.

Dubun dubatar masu adawa da shugaba Mohammed Morsi suna ta shagulgula a dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira, yayin da su kuma magoya bayansa ke gudanar da taron gangami a kusa da wurin, suna masu cewar, za su bijire wa matakin da sojojin suka dauka.

Karin bayani